Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bukaci sabon sarkin katagum daya gudanar da aikisa bisa rikon gaskiya da amana.
Mai alfarma sarkin musulmi ya bayyana haka ne tabakin mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR a wajen bawa sabon sarkin katagum sanda.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace suna fatan mai martaba sarkin Alhaji Umar Farouk zai jogaranci masarautar tasa bissa gaskiya da rikon Amana.
Yayin jawabin godiya Sarkin na Kano Alhaji Aminu Bayero ya godewa dukkanin manyan bakin da suka halarci wannan taro daya gudana a masarautar katagum dake jihar Bauchi.
A nasa jawabin sabon sarkin na katagum Alhaji Umar Farouk ya godewa gwamnatin jihar bauchi bisa irin wannan karamci da dukkanin sarakunan kasar nan suka bashi na halartan bashi sanda da gwamnan jihar bauchi Bala Abdulkadir Muhammad yayi masa.
Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Mai martaba sarkin kazaure Alhaji Najib Husaini Adamu da mai martaba sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bammali da mai martaba Shehun Barno da dai sauran sarakunan kasar nan sun halarci wajan taron.
Sa Hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa sakataren yada labaran masarautar kano