Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa KAROTA ta bayyana shirin ta na cigaba da aiki da Sashen Kula da Binciken Ababen Hawa na (M.T.D) domin sauƙaƙawa matuka ababen hawa.
Jamiin hulda da jama’a na hukumar KAROTA Nabilsi Abubakar Kofar Na’isa shine ya bayyana Hakan ga manema labarai.
Nabilusi yace Shugaban Hukumar KAROTA Hon. Baffa Babba Ɗan’agundi lokacin da yake karɓar baƙuncin sabon Shugaban Sashen Binciken Ababen Hawa SP Abubakar Ibrahim Imam, yace hukumar KAROTA zata yi aiki kafada da kafada da sashin na MTD.
Baffa Babba ya ce Hukumar KAROTA baza ta iya gudanar da aikintaba sai da taimakon Yansanda. A saboda haka ne ya roƙi sabon shugaban da ya ruɓanya ƙoƙarinsa ga al’ummar jihar Kano ƙari akan ƙoƙarin da yake da shi.
A nasa jawabin Sabon Shugaban Sashen Kula da Ababen Hawa SP Abubakar Ibrahim Imam ya bayar da tabbacin aiki tare da Hukumar ta KAROTA domin ciyar da jihar Kano gaba.
Ya bayyana cewa jami’an KAROTA na aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an Sashen domin taimakawa al’umma musamman masu amfani da titi.
Ya ƙara da cewa hadin kan da ke tsakanin jami’an Yansanda da jami’an na karota ne, hakan ya sa ake samun sauƙin cunkoso a titinan jihar nan.
A ƙarshe yayi alkawarin cigaba da ɗora wa kan yadda ayyukan suke tafiya a tsakanin jami’an.