Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace muhimmancin da ruwan sha yake dake dashi abune da yake bukutar kulawa ta musamman.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin sabon kwamishinan ruwa na jihar Kano Alhaji Garba Yusuf Abubakar a fadar sa.
Mai Martaba Sarkin yace duk da cewa sabon kwamishinan ba bako bane a rike irin wannan Matsayi, amma yana da kyakkyawar alaka da fadar masarautar Kano, kuma yana da alaka Mai kyau tsakaninsa da Sarkin tun kafin kasancewarsa Sarkin Kano.
A don hakane Sarkin yace bisa irin kokarin da ya sanshi dashi yayi fatan zai samar da cigaba a Ma’aikatar Samar da ruwan sha ta jihar Kano.
Daya juya ga wadanda suke taimaka masa akan harkar samar da ruwan sha kuwa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi musu nasiha dasu zamo masu gaskiya da amana tareda bayyana masa kuskure idan har ya aikata hakan.
Yace su sani cewa dukkan nasarorin da za’a samu to fa nasarar tasu ce baki daya, inda yayi fatan zasu bada shawarwari nagari domin samun nasarar abunda akasa a gaba.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa Gamnan jihar Kano bisa wannan matsayi daya bashi na kwamishinan Ma’aikatar samar da ruwan sha ta jihar Kano.
Da yake jawabi tunda farko Sabon kwamishinan ruwan Alhaji Garba Yusuf Abubakar yace yazo fadar ne domin neman tubarriki dareda sanya masa albarka a wannan mukami daya samu.
Inda ya bayyanawa Mai Martaba Sarkin cewar zayyi dukkanin maiyuwa wajen ganin ya samar da ruwan sha a jihar Kano inda yace duba da irin hazakar ma’aikatan hukumar ruwa zai sami damar samar da ruwa a jihar Kano.
Alhaji Garba Yusuf ya kuma bukaci Masarautar Kano ta rika bashi shawarwari akan hanyoyin da za’abi wajen magance matsalar ruwan shan a jihar nan.
Magatakardar yada labaran masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa