Daga Walid Hari
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta ceto mutum 27 da aka yi yunkurin safarar su daga Kano zuwa kasashen waje.
Kwamandan hukumar da ke yaki da safarar mutane ta Najeriya reshen jihar Kano (NAPTIP), Abdullahi Babale, ya ce an dauko mutanen ne daga jihohin Oyo da Osun, da Kogi da Ekiti da Legas, da kuma Ogun.
Kuma shekarunsu sun fara ne daga 19 zuwa 40, sannan mata 23 ne sai maza hudu.
Ya kuma kara da cewa masu safarar sun yi yunkurin ketarawa da mutanen ne zuwa Libya don nema musu aiki.
Ya fada wa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, su kuma hada mutanen da yan uwansu.