Kalama Atiku bayan watsi da karar canza shi a matsayin Dantakara da kotu tayi

Kotun Koli, tayi Watsi Da Karar Yunkurin Soke Takarar Atiku ta Shugaban Kasa

Kotun Kolin ta yi watsi da karar da aka shigar a gaban ta kan tilasta was uwar babbar jam’iyyar adawa ta PDP da ta baiwa dan kudancin Najeriya takarar kujerar shugaban kasa.

Hakan ya biyo bayan karar da daya daga cikin yan takaran zaben kujerar kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar jihar Abia, Cosmos Ndukwe, ya shigar kan shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu.

Ndukwe yace rashin baiwa yankin kudu tikitin takarar shugaban kasa karkashin Jam’iyyar PDP ya sabawa kundin tsarin mulkinsu.

Idan zaku iya tunawa uwar jam’iyyar PDP ta baiwa kowani dan yanki damar yin takara a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa inda Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben.

Alkalan kotun kolin sun bayyana cewa an yi watsi da karar ne saboda kotun ba tada hurumin sanya baki cikin harkokin cikin gidan kowacce jam’iyya

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments