Dan takarar Sanatan shiyyar Katsina Ta kudu, Ya bayar da Babura guda 5 domin kara Inganta harkokin tsaro a yankin Malumfashi!!
Dan takarar Sanatan shiyyar Katsina ta Kudu Alhaji Muntari Dan-dutse, Dan majalisa tarayya mai wakiltar mazaɓer Funtuwa Dandume, Honarable Mukhtar Dan-dutse ya aika da baburan hawa guda 5 Domin habbaka tsaro a Yakin Karamar hukumar Malumfashi.
Alhaji Sunusi Hayin gada ne ya mika Baburan ga galadiman Katsina, hakimin Malumfashi Alhaji Saddik Abdullahi Mahuta.
Idan za’a tuna Ƙaramar hukumar Malumfashi ta tsinci kanta cikin matsalar Haraharan Yan bindigan Daji A cikin kwanakin nan.
Ba wannan ne karan farko da Dan Majalisar ke bayar da baburan hawa Domin taimakawa bangaran tsaro ba, ko a shekarar data gabata Alhaji Muntari Dan-dutse ya Bayar da baburan hawa sama da 30 ga ƙungiyar Bijilanti Ta Yankin Funtuwa da Dandume, Domin Kawo karshen Matsalar tsaro a yankin.
Acikin tawagar da suka isar da sakon dan takarar Sanatan akwai Malam iliyasu Umar, Alhaji Mansur abu mai gishiri, Alhaji mati bamba Funtuwa, Alh lado Mai ruwa, Hon.umar ya’u Abba jah Funtuwa DG Dandutse house to house da sauransu, Allah ya kawo mana zaman lafiya