Gwamtin Jihar Kaduna ta karyata radi-radin da ake yadawa na cewa, wai an canzawa jihar suna, daga jihar Kaduna ta kuma jihar Zazzau (Zazzau State)
A wata sanarwa da mai taimakawa gwamna a kafafin yada labarai ta yanar gizo, Muyiwa Adekeye ya rabawa manema labarai a Kaduna, yace mutane su yi watsi da maganar saboda bata da wani tushe ballatana masuma, a dan haka jihar Kaduna tana nan a sunanta na jihar Kaduna.