Masu Sauraronmu Zainab murtala wada ce ke muku sallama ta cikin shirin Murhum Aksam shirin dake kawo muku yadda ake girke-girke na zamani da gargajiya.
A yau zamuji yanda akeyin kunun kwakwa me haske.
Dafari zamu nemi kayan hadi watau ( Ingredients)
Sune kamar haka: Shinkafa
Kwakwa, Gyada, Sugar, Madara
Dafarko zaki sami mazubi me tsafta ki zuba shinkafarki ki wanke ta,se kisami gyadarki ki surfa ta se ki wanke ta tayi tas se ki dakko kwakwarki ki hada da wankakkiyar shinkafarki da wannan gyada kiyi blending dinsu se kidakko abin tatarki me tsafta ki wanke shi ki tace ki ajiye dusar agefe wannan ruwan da kika tace shine zakiyi amfani dashi.
Zaki dakko tukunyarki me tsafta ki juye aciki ki dora akan wuta kada kisa wutar da yawa kiringa juyawa a hankali har yayi kauri,se ki dakko wannan sugar naki kizuba se madararki ta gari ko ta ruwa dik za’a iya amfani dasu.
Wannan shine nau’in kunun kwakwa tare da Zainab Murtala Wada
Ku biyo mu cikin shiri na gaba.