Sanin duk mutumin dake rayuwa ne a wannan zamani yasan ana fama da yawaitar mutuwar aure musamman a kasar hausa duba da hakan ne yasa Dr.mamman dorayi garejin kamilu shugaban cibiyar hada magungunan gargajiya ya bayyana inda gizo ke saka
Daga wakilin aksammedia B.imam
Da farko ya bayyana raba raban dan adam inda ya fara da rabe mana su kamar haka
1.turabi
2.hawa’i
3.al’ma’i
4.annari
1.turabi shine mai yanayin kasa wanda ya tsinci kansa a wannan yanayi shine wanda akafi so bisa dalilin irin saukin mu’amala da yake da ita ga al’umma kuma sunfi yawa a cikin al’umma.
2.hawa’i shine mai yanayin iska wanda ya kasance a wannan aji to shine a cikin al’umma yafi yawan fishi.
3.al’ma’i wannan shine mai yanayin ruwa mai wannan yanayin jikin sa yana daga bangaran danyan taka shikam akwai yawan rashin lafiya
4.annari wannan shine mai yanayin zafi a cikin al’umma shi wannan yana da yawan jin zafi a jikin sa halayyar sa kuma akwai saurin daukar zafi
Abinda ya kamata in an tashi aure a hada wannan jinsi da jinsi domin aure ya zauna lafiya
In san samu ne a hada:
Turabi da hawa’i wannan hadin shine in aka hada ana zaman lafiya da juna za’a zauna ciki lafiya baka lafiya
Ma’i da nari haka zalika wannan hadi in aka samu daidaito na aure za a zauna salamun salamun
Daga karshe Dr.mamman dorayi garejin kamilu shugaban cibiyar hada magunguna yana yiwa ma’aurata fatan Alkhairi
Domin karin kayani 08060250051 ko 09025296907