A jiya Litinin ne aka bude dandalin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka, wato makon musayar ra’ayoyi kan hadin gwiwar al’adu a tsakanin Sin da Afirka a birnin Jinhua na lardin Zhejiang na kasar Sin.
Mataimakin shugaban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa na kasar Sin, kana shugaban kungiyar hadin gwiwar masana’antu da cinikayya ta kasar, Gao Yunlong, ya halarci bikin bude taron, inda ya gabatar da jawabi. Cikin jawabin nasa, Gao ya ce, “Sin da Afirka suna goyon bayan juna, suna kuma taimakawa juna, lamarin da ya sa suka samu sakamako da dama, bisa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban”.
Ya ce, yanzu haka an bude wani sabon babi ta fuskar hadin gwiwar Sin da Afirka, ana kuma fatan za su tsaya tsayin daka a fannin habaka harkokin kirkire-kirkire, da kuma inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya zuwa wani sabon matsayi.
Haka kuma, ya ce, ana sa ran karfafa mu’amalar al’adu da jama’a a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, domin zurfafa zumuncin dake tsakanin al’ummomin bangarorin biyu, kana, ana sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin, don su sauke nauyin dake wuyansu, da kuma ba da karin tallafi ga al’ummomin nahiyar Afirka.