Jaridar “The Punch” ta ruwaito wani bayani daga asusun ba da lamuni na duniya wato IMF a jiya na cewa, ya kamata kasar ta shirya fuskantar kalubalen hauhawar farashin abinci a shekarar 2023.
Kuma, bisa rahoton da hukumar kididdiga ta kasar ta fitar, a watan Oktoban bana, adadin hauhawar farashin abinci ya kai kaso 23.72%, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin na shekarar bara, inda adadin hauhawar farashin wasu kayan abincin musamman ya kai 50% zuwa 100%.
Bugu da kari, asusun IMF ya bayyana cewa, a shekarar 2023, farashin abinci a kasar Nijeriya zai ci gaba da karuwa.
Ban da bala’in ambaliyar ruwa, da karuwar farashin takin zamani, sauyawar darajar kudin Naira, da gibi mai yawa na kasafin kudin gwamnatin tarayyar Nijeriya da kuma sauyin yanayi, dukkansu, sun haddasa hauhawar farashin abinci a kasar.