Kungiyar kasuwar abinci ta Duniya dake kasuwar Dawanau a karamar hukumar Dawakin Tafa, ta nesanta kanta da wani rahoto da ake yadawa cewa: an kama wani dankasuwar da buhunhunan fulawa gurbatattu sama da Dari hudu.
Sakataren kungiyar kasuwar Kwamaret Rabiu Abubakar Timfafi ne, ya bayyana haka ga manema labarai a nan jihar Kano.
Yace, yadda abin ya faru wani dankasuwar ne,ya baiwa wani dankasuwar Singa aron gurin ajiyar kaya,wato,store domin ajiye kayansa,sakamakon, haka ashe hukumar kare hakkin mai siye da mai siyarwa ta samu rahoto dangane da fulawar gurbatacciya ce,inda suka,kama kayan.
Amma,shugabancin kungiyar kasuwar karkashin jagorancin Alh muttaka Isah,ya kirawo Shugaban kungiyar kasuwar Singa, domin jin ba,asin akan lamarin Wanda, ya tabbatar da cewar dankasuwarsa ne,tare da shiga lamarin.
Yace,kuma,ita kanta hukumar data kama fulawar ta tabbatar da kasuwar Dawanau ba,a sana,ar fulawa,sai Dai a kasuwar Singa, inda kuma,Kwamaret Rabiu Abubakar Timfafi, daya yi jawabi a madadin kungiyar kasuwar,ya kara barranta kasuwar Dawanau da gudanar da irin wannan ko makamancin haka, domin al,umma su fahinta ba,a kawo gurbatattun kayayyaki zuwa kasuwar Dawanau.
Haka zalika, yace, kungiyar kasuwar Dawanau ba za ta laminci wani dankasuwar ko bako ya shigo mata kayayyaki da basu da inganci ko kuma,gurbatattu domin yin kasuwanci ba,inda tace,duk Wanda ta kama,to zata kamashi tare da mikashi ga hukumomin dake da alhaki akan haka domin hukuntawa,kamar yadda doka ta tanada.
Daga karshe Sakataren kungiyar kasuwar Kwamaret Rabiu Timfafi, yace, shugabancin kasuwar Dawanau ya fito da wasu dokoki ga duk Wanda zai shigo da kayayyaki sai kungiyar kasuwar ta San ingancinsa kafin a shigo su,domin gujewa batagari da sauran marasa gaskiya.