A Yau Ne Makarantar Bara’u Ibrahim Memorial Schools (BIMS) Dake Akan Titin Shehu Idris, Kabala Dai-dai Filin Shanya, Tudun Wada a Karamar Hukumar Kaduna Ta Kudu, Jihar Kaduna
Ta gudanar da bikin walimar saukar karatun Al’qur’an Mai Girma, gami da karrama wasu al’umma da suke bada gunmawarsu domin cigaba da ilmantar da ‘yan ‘yansu
To farko da yake jawabi shugaban taron wanda kuma shi ne Babban Daraktan Ayyuka na Musamman a Kwallejin Kimiya Da Fassaha Ta Gwabnatin Tarayya dake Kaduna Dakta Muhammad Suleiman, ya ja hankalin dalibain da su zamantu jakadu nagari a duk inda suke, sannan yan zo wani suka sa danba wajan naiman ilimin Addinin da Boko
Shi kuwa Limamin Masallacin Juma’a Na Hayin Dan Mani dake Karamar hukumar Igabi Sheikh Musa Yahaya, ya fadi kadan daga cikin falalar saukar karatun Al’qur’an Mai Girma inda ya kawo ayoyi da hadisai
Haka kuma, shima uban kasa Hakimin Tudun Wada, Sarkin Ruwan Zazzau Alhaji Tahir Muhamud, Wanda Sarkin Kinkinau Alhaji Ahmad Rufa’i Abdullahi Bamali ya walinceshi ya nuna godiyarsa ga wanda ya hassasa wannan makaranta wato Marigayi Alhaji Bara’u Ibrahim
Malam Abu Safiyyanu Abdullahi, shi ne Shugaban Makarantar yace wannan ranar, ranace mai matukar tarihi saboda wannan shi ne karan farko da makarantar da fara yaye dalibanta
Acewar daya daga cikin ‘ya ‘yan wanda ya assasa Makarantar kuma Jagoran kula da Makarantar Alhaji Abdullahi Mai Kano (Bara’u) yace wajibine iyaye su reka bibiyar abubuwan da ake koyawa ‘ya ‘yansu, sannan ya bayyana farin cikinsa bisa yarda Makarantar take dauka yara marayu da marasa galihu domin yin karatu Kyau a duk shekara ba tare da sun biya ko sisi ba. Kimanin Dalibai 87 suka sauke Al’qur’anin.