Kasar Nijar tarabauta da tallafin Dala miliyan 3 daga Gidauniyar BUA

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya karbi bakuncin ayarin ‘Yan kasuwar Najeriya da suka ziyarce shi a birnin Yammai, a karkashin jagorancin shugaban kamfanin BUA Abdusamad Rabiu.

Shugaba Bazoum tare da tawagar Abdusamad

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar su da shugaba BAzoum, Rabiu yace sun kai ziyarar ce domin bunkasa dangantaka da kuma hadin kai tsakanin kasashen biyu.

Kazalika sun tattauna batutuwan da suka shafi kasuwanci da zuba jari tsakanin kasar Najeriya da Nijar musamman ganin irin matsalolin da duniya ke fuskanta yanzu sakamakon illar da yakin Ukraine ya haifar.

Shugaban kamfanin na BUA wanda kuma shine shugaban kungiyar Yan kasuwan kasashen Faransa da Najeriya yace suna shirin fadada dangantaka tsakanin kamfanin siminitin su dake Sokoto a bangarorin biyu, tare da duba wasu fannonin kasuwancin da zai shafi kasashen.

Rabiu yace wannan dalilziyarar su da kuma ganawa da shugaba Bazoum domin yi masa bayani akan ayyukan da suke yi da kuma bukatar taimakawa juna ta hanyoyin da suka kamata.

Daga bisani shugaban kamfanin BUA ya sanar da bada tallafin Dala miliyan 3 daga gidauniyar sa dake taimakawa kasashen Afirka domin bunkasa ilimi a Nijar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments