An saka gawar Sarauniya cikin taskar adana gawa.
Walid Hari
An saka gawar Sarauniya cikin taskar adana gawa, gabanin binne ta
Daga nan sai babba sarkin yakin fadar wato Garter King of Arms, ya ambaci salo da sarautun da ake kiran Sarauniyar lokacin mulkinta.
Nan gaba kadan ne da maraicen nan iyalan gidan sarautar Birtaniya za su binne gawar Sarauniya Elizabeth ll, tare da mijinta Yarima Philip Duke na Edinburgh, a wani daki da ake kira ‘King George VI’, wanda ke cikin cocin St George
Za kuma a rubuta ELIZABETH II 1926-2022 a kan kabarinta, domin nuna tsawon lokacin da ta rayu a duniya
A dazu ne dai aka gudanar da jana’izar kasar ga Sarauniyar, wadda shugabannin kasashen duniya daban-daban suka halarta.