Wata Matar Aure mai suna Zakkiya Isyaku Dake Unguwar Garin Kawa a Karamar Hukumar Kura tayi ta maza yayin da taji alamun motsin mutane da tsakiyar dare a gidan ta.
Daga Dantala Uba Nuhu Kura
Matar bayan jin motsin da tayi ba tayi wata-wata ba sai ta fito domin ta ganewa idanuwan ta ko maye yake faruwa fitowar tata ke da wuya ta arba da wasu mutane Uku da Sukaje Satar Wani Kasur-Gumin Sa a Cikin gidan nata
Duk da yake San na Kanin Mijinta ne Maisuna Isa Isyaku Da Yake Kiwo a Gidan nata Zakiya Bata tsaya wasa ba inda ta tunkari barayin shanu kuma tayi nasarar Korar su.
Barayin sun Sami Nasarar Kwwnce I Giya San Daga Jikin Turken San anna Cikin Ikon Allah Zakiya tayi kukan Kura Inda Suma Suka Kaimata Wabta Da Duka Da Kutufo Suka Kuma Cika Rigarsu Da Iska
Saidai Tuni Ta Sheda Guda Daya Daga Cikinsu Wanda Yasa Kafa Ya Shureta a Cikin Daren Ta Fadi mai Suna Isyaku Munkaila dake Yankin Garin Nasu Na Kawa a Karamar Hukumar Kura
Da gari yawaye tuni aka Sanar da ofishin yan sanda kuma aka kamo Isyaku
Bayan Yan Sanda Sun Kammala Bincike Suka Kuma Tura Gaban Kotun Shariar Musuluncin Ta Kura Mai-Sharia Malam Ibrahim Isa Usman yake jagoranta.
Bayan Maigabatar Da Kara Insifecta Nasiru Dan-Sakkwato Ya Mike Ya Kuma Karanta Takardar Tuhuma Nan Take Wanda Ake Zargin yace Bai Aikataba
Nan Take Maisharia Malam Ibrahim Isa Usman Yacewa Maigabatar Da Kara Kaji Yaki Amsawa
Maigabatar Da Kara Yace Daman Suma Suna Da Ragowar Bincike
Sannan aka Daga Shariar Zuwa 21/9/2022
Tuni Alkalin Kotun Maisharia Malam Ibrahim Isa Usman Ya Dan-‘Kashi Hanun Jamiin Gidan Ajiya Da Gyaran Hali Insifecta Awwalu Muhammad Alasan Danhasan zuwa waccan rana da aka ambata.