KOTU TACI TARAR ABDULJABBARU TARAR NAIRA MILIYAN GOMA (10)
Walid hari
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau Litinin ta ci tarar malamin addinin Musulunci da ake tsare Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, Naira Miliyan 10 bisa shigar da kara kan tabbatar da hakkinsa na ɗan ƙasa, inda kotun ta ce hakan rashin ɗa’a ne ga kotun.
Mai shari’a Emeka Nwite a cikin hukuncin da ya yanke ya bayar da umarnin a biya wadanda ake kara kudaden da su ka haɗa da Kotun Shari’a ta Kofa Kudu, Kano, da gwamnatin jihar Kano a matsayin waɗanda a ke kara na daya da na biyu.
Mai shari’a Nwite ya kuma baiwa Kabara da lauyansa Shehu Dalhatu umarnin su biya gwamnatin jihar Naira dubu 100.
Alƙalin kotun ya ce da zarar kotu ta gamsu cewa an saɓawa tsare-tsaren kotu wajen shigar da ƙara, to kotu na da hakkin hukunta wanda ya shigar da karar.
Ya ce matakin da lauyan Kabara ya dauka na nufin samun hukuncin da ya dace ko ta halin kaka.
Nwite ya ce shigar da kara a cikin wata kara mai lamba: FHC/KN/CS/185/2022 a Kano da kuma zuwa Abuja