Tsohon shugaban kasa na mulkin soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ja hankalin al’ummar kasar nan da su ci gaba da hada kai domin Najeriya ta ci gaba da kasancewar a matsayin kasa guda.
Babangida ya yi jan hankalin ne a zantawa sa da manema labarai a lokacin murnar cikarsa shekaru 81 a duniya ya ce hakuri shine babban abinda ya kamata ‘yan Najeriya su rike domin cin moriyar juna duk da banbancin yare da addini dake a tsakanin al’ummar Najeriya.
A fannin tsaro da ya addabi sassan kasar nan kuwa babangida ya ce a ci gaba da addu’a kuma akwai lokacin da lamarin zai zama tarihi ga kasar nan.