Daga fadar masarautar jihar kano

Mai Martaba Sarkin Kano Allhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci da al’umma da su sabinta katin tukin ababan hawansu domin gujewa afkuwar hadura.
Sarkin yayi kiran ne lokacin da shugaban hukumar karbar haraji ta jihar Kano ya kawo Masa ziyarar bashi katin shedar tukinsa da yayi a watan da ya huce

Alhaji Aminu Ado Bayero,ya ce katin shedar tukin Yana da mutukar mahimmanci ga al’ummar kasar nan.
Ya kuma yabawa hukumar kare afkuwar hadura ta kasa da hukumar karbar haraji ta jihar Kano dongane da kokarin da suke da shi na samarwa da al’umma katin shedar tukin ababen hawa.

Daga wakilin aksammedia B.imam

Dayake jawabi shugaban hukumar karbar haraji ta jihar Kano Abdurrazaq Datti salihi ya yabawa masarautar Kano da irin kokarin da take wajen fadakar da al’ummar jihar nan.

Shima a nasa jawabin shugaban ma’aikata na hukumar kiyaye hadaruka ta kasa Hafiz Muhammad Tarauni yace ya zo Kano ne domin mikawa mai Martaba sarki katin shedar tukisa da yayi

kwammandan hukumar kiyaye haduruka ta kasa reshin jihar Kano Zubairu Mato yace hukumar su tana kokari wajen ganin anyi tuki cikin kwanciyar ankali.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments