Rundunar sojin ruwan ta harba makaman mai ketare iyakokin kasashe zuwa tekun Pacific daga sansaninta na Vandenberg da ke jihar California a cikin duhun dare.
Makamin mai linzamin na dauke da wani kumbo wanda ake iya cusa masa wani makamin nukiliya a cikinsa musamman a lokacin yaki domin kaddamar da farmaki.
Kumbon dai ya yi tafiyar tsawon mil dubu 4 da 200 zuwa Kwajalein Atoll da ke tsibirin Marshall a can yankin yammacin tekun Pacific.
Rundunar sojin ruwan Amurkar ta ce, gwajin makamin na a matsayin wani bangare na ayyukan da ta saba gudanarwa lokaci zuwa lokaci, amma a wannan karon ta yi hakan ne domin nuna cewa, har yanzu makaman Amurka na dakile hare-hare na nan daram cikin aminci da inganci.
Rundunar ta ce, ta gudanar da gwaje-gwajen makamai fiye da sau 300 a can baya, amma kuma gwajin na baya-bayan ba shi da alaka da abubuwan da ke faruwa yanzu haka a duniya a cewarta.