Adadin mutanen da suka mutu a rikicin Koriya ta kudu ya karu izuwa 156

Akalla mutane kimanin 156 sun rasa rayukan su sanadiyar wani mummunan rikici da ya barke a kasar Koriya ta kudu.

Mummunan lamarin ya afku ne a ranar Asabar a gundumar Itaewon na babban birnin kasar, Seoul, a yayin shagalin Bikin Halloween inda jama’a suka tarwatse cikin rikici.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Yawancin wadanda abun ya shafa matasa ne sai kuma mutane 26 daga cikinsu ‘yan kasashen waje ne.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments