Gwamnatin kasar Habasha da mayakan yankin Tigray, sun amince da dakatar da bude wuta a jiya Laraba, bayan gudanar da shawarwari a birnin Pretoria na Afirka ta kudu.
Wata sanarwar hadin gwiwa da sassan biyu suka fitar, kuma kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi, ta ce yarjejeniyar dakatar da bude wutar, ta kawo karshen tashin hankalin da sassan 2 suka kwashe shekaru biyu suna kwabzawa a yankin arewacin Habasha.
Game da hakan, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ja hankalin gwamnatin Habasha, da sauran sassan kasa da kasa da su mara baya ga yarjejeniyar. Cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, Mr. Guterres ya yi na’am da cimma wannan matsaya. Yana mai cewa, matakin ya cancanci yabo, kuma hakan muhimmin jigo ne na kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe shekaru 2 ana yi, wanda kuma ya haifar da asarar rayuka da dama.
Mr. Guterres ya kuma bayyana goyon bayansa ga matakin aiwatar da yarjejeniyar, yana mai kira da a ci gaba da tattaunawa kan sauran batutuwan da suka rage, ta yadda za a kai ga kawo karshen duk wani sabani, da cimma matsayar siyasa mai dorewa, da kawo karshen jin amon bindigogi, tare da mayar da Habasha kan hanyar zaman lafiya da daidaito.