Borussia Dortmund na iya bukatar a biya ta fam miliyan 130 kafin ta saki Jude Bellingham, dan wasanta na tsakiya mai shekara 19, wanda kungiyoyin gasar firimiya kamar Manchester United da Chelsea da Liverpool ke ribibin dauka.(Sun)
Mai tsaron gidan kungiyar Sfaniya David de Gea mai shekara 31 zai amince a rage albashinsa na fam 375,000 wanda Manchester United kan biya shi a kowane mako domin ya tsawaita zamansa a Old Trafford. (Athletic, via Sun)
Chelsea na kan gaba cikin kungiyoyin da ke son daukan Adrien Rabiot, dan wasan tsakiya na Faransa mai shekara 27, da zarar an bude kasuwar ‘yan wasa a watan Janairu. (Fichajes – in Spanish)
Everton da Newcastle United kuwa na sa ido kan Armano Broja, dan wasan gaban Chelsea da Albaniya mai shekara 21. (CBS Sports)
Unai Emery ya sanya hannu kan kwantiragin zama kocin Aston Villa na tsawon shekara hudu da rabi, kuma babu kocin da ya taba yin haka a tarihin kungiyar. (Telegraph – subscription required)
Chelsea ta yi yunkuri na fam miliyan 30 domin sayo Leandro Trossard, dan wasa gaba na Brighton da Belgium mai shekara 27. (FourFourTwo)
Barcelona na tunanin raba Mikel Arteta mai shekara 40 da kungiyarsa ta Arsenal domin ya karbi ragamar horas da ‘yan wasan kungiyar a Camp Nou, domin ya maye gurbin koci mai-ci Xavi Hernandez mai shekara 42. (Sport)
Har zuwa wannan lokaci, Toni Kroos, dan wasan tsakiya na Jamus mai shekara 32 bai yanke hukunci kan tsawaita zamansa a Real Madrid ba. (ESPN)
Fatan da Arsenal da Chelsea ke yi na sayo Wilfried Zaha daga Crystal Palace ta karu, yayin da dan wasan mai shekara 29 ya ki amincewa da tsawaita zamansa duk da tayin da aka yi masa mai gwabi. (Mail)
Leeds United za ta saurari kungiyoyin da ke son sayen dan wasanta Adam Forshaw mai shekara 31 amma sai nan da watan Janairu mai zuwa. (Football Insider)