Sabbin alkaluman da gwamnatin Najeriya ta fitar, sun nuna cewar, sama da mutane 600 suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwan daminar bana a Najeriya, wadda ke zama mafi muni cikin shekaru goma.
Ma’aikatar ayyukan jin kai ta Najeriya ce ta wallafa sabuwar kididdigar a shafinta na Twitter, inda ta ce ambaliyar ruwan ta tilastawa sama da mutane miliyan 1.3 barin gidajensu.
Ministar kula da ayyukan jin kai ta Najeriya Sadiya Umar Faruq, ta ce mutane 603 suka mutu yayin akuwar iftila’in. in ji ministar agajin jin kai Sadiya Umar Farouq.
Ya zuwa yanzu dai, ambaliyar ta lalata gidaje sama da 82,000 da kuma gonakin da fadinsu ya kai kusan kadada 272,000.
A shekarar 2012, mutane 363 ne suka mutu yayin da wasu sama da miliyan 2.1 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwan.