Yan Daba Ɗauke da Makamai Sun Kai Hari Wurin Gangamin Taron Atiku a Kaduna
Kaduna – Rahoton da muke samu ya nuna cewa wasu yan Daba sun faramki magoya bayan PDP a Ranches Bees Stadium, Kaduna, wurin gangamin taron ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya tabbatar da faruwar lamarin a wani rubutu da ya saki a shafinsa na dandalin Facebook ranar Litinin.
Atiku ya yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da ya umarci sauran jam’iyyu su dakatar da mambobinsu daga yunkurin ta da yamutsi a wurin taron.