Benzema ya lashe kyautar Ballon d’Or a karon farko.
Dan wasan Real Madrid, Karim Benzema ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya da ake kira Ballon d’Or.
Benzema ya ci kwallo 44 a wasa 46, wanda ya bayar da gudunmuwar da Real Madrid ta lashe La Liga da Champions League a 2021/22.
Yar wasan Barcelona, Alexia Putellas ce ta sake lashe gwarzuwar kwallon kafa ta duniya ta 2022.
Manchester City, wadda take da ‘yan takara shida ta lashe kyautar kungiyar da ba kamarta.
An bayar da kyautar bana bisa kwazon dan wasa a kakar 2021/2022, maimakon shekara daya da ake yi a baya.
Zidane ne ya lashe kyautar 1998, kuma shi ne ya bai wa Benzema kyautar bana.
Lionel Messi mai rike da kyautar bara mai bakwai jumulla da Cristiano Ronaldo mai biyar, sun lashe 12 daga Ballon d’Or 13 baya.