gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar warware takaddamar dake tsakanin ta da kungiyar malaman jamioin kasar nan wanda yayi sanadiyar shigar su yajin aiki fiye da watanni biyu da suka wuce.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta bakin Ministan yada labarai na Kasa, Lai Muhammad, inda yace duda bukatun ba masu sauki bane.
Muhammadyace gwamnati ta damu matuka da yadda dalibai suke zaune A gida wanda hakan babban nakasu ne ga karatun daliban.