Shugaban Kamfanin mai na kasar Rasha, Alexei Miller, ya ce kasar su ita take da alhakin tsara yadda suke so su sayar da makamashinsu, saboda haka ba sa bukatar katsalandan daga wata kasa domin su suka mallaki dukiyarsu.
Yayin da yake tsokaci dangane da rage yawan iskar gas din da suke tura wa kasar Jamus, Miller ya shaida wa mahalarta taron tattalin arzikin da ke gudana a St.Petersburg cewar, ba sa amfani da dokar da ba su sanya hannu akai ba, saboda haka dole ne kasashen duniya su yi amfani da dokokin da suka shata wa kansu.
A farkon wannan mako,kamfanin Gazprom ya rage yawan iskar gas da yake aika wa kasar Jamus ta bututun ‘Nord Stream’, saboda abin da ya kira gazawar kamfanin Siemens na kammala gyaran tashar daskarar da iskar.
Miller ya ce ya zuwa yanzu babu hanyar warware matsalar da ta taso ta tashar daskarar da iskar, yayin da kamfanin Siemen ya ki cewa komai akan lamarin.
A Alhamis din nan, Kamfanin Gazprom ya ce ya rage tura iskar gas ga kasashen da ba sa cikin Tsohuwar Tarayyar Soviet da kusan kashi 30 daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Yuni.
Takaddama tsakanin Rasha da kasashen yammacin duniya da ke sayen makamashi daga wurinta, ya yi kamari, saboda matakin da ta dauka cewar dole a rika biyan ta da kudin Ruble maimakon Dala.
Wannan ya sa Rasha ta daina sayar wa kasashen da suka bijire wa matsayinta biyan makamashin da kudin Ruble cikin su har da Poland da Bulgaria da Finland da kuma Netherlands