Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara jihar Kano domin yin ta’aziyyar rasuwar dan sanata Kabiru Gaya da ya rasu a makon nan.
Daily Trust ta ruwaito Osinbajo ya ce Sadiq Gaya, da ga sanatan kamar da yake a wurinsa, inda ya bayyana jimamin rashinsa
Kuma ya bayyana jimami da ta’aziyyarsa da ban hakuri ga iyalan sanatan bisa babban rashin Dan sa
Osinbajo ya ce “Wannan ziyara ce mai matukar ban takaici. Sadiq matashi ne. Kamar da yake a wurina. Ya ziyarce ni sau da yawa. Lauya ne shima kamar dai ni. Don haka, ina da alaka mai karfi dashi.
“Na yi matukar jin wannan rashin. Ina mika ta’aziyyata ga ga sanata da dukkan iyalansa, gwamnati da al’ummar jihar Kano bisa wannan rashi da wannan da mai matukar daraja.