Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin sun rike gawar yarinya mai shekaru 12 saboda iyayenta sun gaza biyan N400,000 na maganinta
Mahaifin yarinyar yace, ya roki asibitin amma sun kammala gawarta a wurinsu har sai sun biya bashin inda yace bashi da hanyar samun wadanda kudaden saboda ciwon da yarinyar tayi ya cinye musu ‘dan kudin da suka samu
Kamfanin Dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa yarinyar ta mutu a asibitin run ranar 15 ga watan Yuli yayin wata jinya da tayi.
Yace, dukkan kudin da ta sha magani zuwa na kwanciya asibitin ya kai N400,000.