Zalincin shugabanni ne yake cire wa talakawa shaawar yin zabe: Hukumar Kare hakkin dan Ada
Anyi kira ga daukacin al’umma da su fito kwansu da kwarkwata suyi katin zabe domin ta hanyar sane zasu zabi wanda suke ganin zai tsamo su daga wahalar da ake fama da ita a wannan kasa.
Daga B. Imam
Kiran ya fito ne Daga Daraktan gamayyar kungiyoyin Kare hakkin Dan Adam na jihar Kano, Kwamaret Karibu Yahya Lawan Kabar, a zantawar sa da wakilin Aksammedia Abdurashid Bello Imam.
Kabara yace a yanzu ne yafi cancanta ga kowa mutum musamman Dan Arewa da ya mallaki katin zabe duba da yadda siyasar ta zama bangarori biyu ne suke dama ta kuma masu adawa da juna.
Kabara ya Kara da cewa yanzu lokaci ya wuce da masu madafun iko zasu rika yin amfani da kujerar su ta hanyar yin magudin zabe kamar yadda aka yi a baya a wasu jihohin dama matakin kasa.
Kazalika ya ce kungiyoyin Kare hakkin Dan Adam a shirye suke su saka ido akan dukkanin zaben da za a gudanar a kowanna mataki na kasa da ya jihohi.