Ministan sadarwa Farfesa Isah Ali Pantami, yace saboda kokarin da yake yi wajan ganin yasauke nauyin aikin da aka dora masa baya yin bacci na mintuna sittin a cikin awa ishirin da hudu.
A S Gwammaja
Wani lokaci dana yi Sallar Ishsha idan na shiga bana taba runtsawa sai an yi Sallar asubahi, Kai wani lokaci a sati daya bana iya yin bacci minti sittin;inji Pantami
Dukkan wanda yake aiki da ni zai tabbatar maka da haka saboda wani lokaci suma ina hana su bacci saboda yana yin aiki karfe 1 na dare ma nakan turawa daya daga cikin su aiki a yanar gizo ya gama ya dawo mun da shi, a wasu kwanakin ma bana taba samun baccin awa biyu a cikin awa ashirin da hudu.
Ina yima Allah godiya, aikin da muke yi daidai gwargwado mun fahimce shi, shi na karanta a digirina na farko haka dukkan digiri na biyu sau biyu nayi Kuma duk a kan haka Kuma digirina na uku a kan sa ne banda sauran karance karance da nayi duk a kan fasahar zamani.
Daga lokacin dana shiga ofis bana tunanin na kai kwanaki talatin na gama kammala dukkan tsarin da zai tafiyar da maaikatar bama kawai iya lokacin da zan kammala aiki ba har zuwa 2030; inji Pantami