Yan tawayen M23 na cigaba da mamaya a kasar Congo

RelatedPosts

An sake gwabza kazamin fada a Jamhuriyar Demokradiyar Congo ranar Lahadi, bayan da ‘yan tawayen M23 suka sake kai wani sabon hari kan sojoji a garin Bunagana da ke gabashin kasar.

Damien Sebusanane, shugaban wata kungiyar farar hula na yankin ya ce galibin al’umma sun tsere daga tsakiyar Bunagana, dake zama muhimmiyar hanyar jigilar kayayyaki a kan iyakar kasar da Uganda.

An sake samun barkewar fada tsakanin sojoji da ‘yan tawayen M23 a yankin, wanda gwamnatin kasar ta dora alhaki kan makwabciyarta Rwanda. Sai dai Rwanda ta sha musanta goyon bayan kungiyar ‘yan tawayen.

An kai wa sojojin hari ne da safiyar Lahadi a Bunagana da kuma garin Tshengerero da ke kusa, dukkansu a lardin Kivu ta Arewa, in ji wani jami’in soji na yankin Kanar Muhindi Lwanzo.

Sebusanane ya ce mayakan na M23 sun yi wa Bunagana kawanya, kuma tankokin sojin Congo suna ta luguden wuta a kan ‘yan tawayen daga cikin garin.

Wani jami’in sojan da ya ki bayyana sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, sojojin kasar Congo suna fatattakar ‘yan tawayen, inda ake ci gaba da gwabza fada a kan hanyar Bunagana.

RelatedPosts

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments
Kasar Amurka ta amince da Kara rura wutar rashin zaman lafiya tsakanin Isra’ila da abokan adawarta

Kasar Amurka ta amince da Kara rura wutar rashin zaman lafiya tsakanin Isra’ila da abokan adawarta

Wani jami'in Amurka ya tabbatar wa kafar yada labarai ta BBC cewa ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta sanar wa majalisar ...

Sojojin Cameroon sun fuskanci mummunan hari daga Yanbindiga

Sojojin Cameroon sun fuskanci mummunan hari daga Yanbindiga

Jami'ai sun ce ƴanbindiga sun kashe sojojin Kamaru aƙalla shida a wani hari da suka kai kan iyakar ƙasashen biyu. ...

Jawabin shugaban kasar Sin, Xi Jinping na sabuwar shekarar 2025

Jawabin shugaban kasar Sin, Xi Jinping na sabuwar shekarar 2025

’Yan uwa da abokai, maza da mata, barka dai. Lokaci na gudu cikin sauri, kuma sabuwar shekara na gabatowa. Ina ...

Kasar Ivory coast ta bi sahun Niger ta yanke alaka da Faransa

Kasar Ivory coast ta bi sahun Niger ta yanke alaka da Faransa

Sannu-sannu dai Faransa na ci gaba da rasa tasirin da take da shi a wannan yanki na Afirka ta Yamma, ...