Kasar China tace za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta hana Taiwan samun ‘yancin gashin kanta, matakin da ke kara rurura wutar rikici tsakaninta da Amurka kan yancin tsibirin.
Ministan tsaron kasar China ya sha alwashin me a jiya Lahadi, yana mai cewa kasar baza ta amince ba har sai inda karfinta ya kare.
Amurka da China na musayar kalamai kan tsibirin mai cin gashin kansa, wanda Beijing ke kallonsa a matsayin wani yankinta dake jiran sake hadewa.
Kutsawar jiragen saman kasar China kusa da yankin Taiwan ya kara dagula yanayin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu masu karfin fada aji.