Yan Sanda Sun Ceto Mutane Hudu daga hanun masu garkuwa da mutane a Jahar Kaduna

 

Inda mutum ɗaya ya rasu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna.

An bayyana sunan wanda aka kashe da Yarima Mohammed mazaunin Kufena, wanda ya yi wa maharan turjiya lokacin da suka nemi yin garkuwa da shi.

Wata sanarwar ‘yan sanda da kafofin yaɗa labarai suka ruwaito ta ce jami’an tsaro sun bi sawun maharan tare da ceto mutum huɗu.

Kakakin rundunar a Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce maharan sun far wa garin Gabari da ke yankin Samaru na Sabon Gari cikin kakin soja ɗauke da manyan makamai, inda suka dinga harbi kan mai tsautsayi kuma suka yi awon gaba da mutum huɗu.

A cewarsa, rundunar ta yi nasarar ceto mutum biyu daga cikin mutanen bayan dakarunta sun yi wa ‘yan fashin kwanton-ɓauna.

Irin wannan salon dakarun suka bi a ƙauyen Gwada inda suka yi nasarar ceto sauran mutum biyun da aka sace tare da taimakon mayaƙan sa-kai, waɗanda suka far wa ‘yan bindigar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments