Kano pillars na fuskantar kalubale

Biyo bayan lokaci mai tsawo da Kano pillars ta shafe tana buga wasanni a filayen wasa na aro ayau yan wasan Kano pillars sun fuskanci kalubale sakamakon wasan da suka buga da Katina United a birrnin katsina.

 

Kamar yadda wakilin Aksammedia Hassan Umar Gwammaja ya sami zantawa da ganau sun sheda masa cewa bayan kwashe mintuna 86 kowa na nema ne sai rikici ya barke tsakanin kulablukan biyu wanda yayi sanadiyar tashi wasan batare da an kammala ba.

 

Pillars ta jima tana fuskantar matsaloli musamman a wannan kakar wasan na firimiya wanda ta fara buga wasan ta na gida a garin Kaduna amma sakamakon tsangwama suka kaura suka koma jihar katsina.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments