Yan bindiga a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun kashe ‘yan sa kai fiye da 30 a wata musayar wuta tsakanin bangarorin biyu cikin wani yanki na karamar hukumar Bungudu da ke jihar.
Daga Lauwali Gusau
Rahotanni sun ce a litinin din da ta gabata ne‘yan bindigar suka farmaki garin Auki da ke karamar hukumar Bungudu wanda ya kai ga fito na fito tsakaninsu da ‘yan sa kai da ke bayar da tsaro ga al’ummar yankin wanda ya kai ga kisan mayakan sa kan fiye da mutum 30 a cewar shaidun gani da ido.
Jaridar Daily Trust ta Najeriyar ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun hallaka wasu daidaikun fararen hula a kauyen gidan dan Inna da sauran kananun kauyukan da ke gab, ko da yak e ba a samu hakikanin alkaluman wadanda suka rasa rayukansu a farmakin ba.
A cewar jagoran mayakan sa kan da ke jihar ta Zamfara, tun farko ‘yan bindigar sun harbe wasu makiyaya tare da kora shanunsu dalilin da ya sanya su ankarar da ilahirin ‘yan sakan da ke makwabtan kauyukan wadanda suka hadu tare da cimmusu.
Sai dai a cewar wani mazaunin yankin Umar Kadowa bayan wannan dabara ta ‘yan sa kai da ya kai ga yiwa ‘yan bindigar a tara-a tara ne sai suka rabu gidan biyu da yadda kashin farko suka ci gaba da kora shanun yayinda sauran suka tsayawa don musayar wuta da ‘yan sa kan.
A cewar Kadowa, adadin ‘yan bindigar ya ninka adadin ‘yan sakan haka zalika suna rike da makamai wanda ya sanya suka iya kashe ‘yans akan fiye da 30