Du Dan takarar da jam’iyar APC da PDP zasu tsayar basa gabana: kwankwaso

A yau Talata 31 ga watan Mayu jam’iyyar NNPP ta tantance ɗan takarar shugaban ƙasarta injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala tantancewar, Sanata Kwankwaso ya ce bai kai ga tsayar da wanda zai zama mataimakinsa ba tukunna.

Ya ce sai bayan an yi babban taron jam’iyyar na ƙasa sannan masu ruwa da tsaki na NNPP za su haɗu a yi shawarar wanda zai yi masa mataimaki a takarar.

Kazalika Kwankwaso ya ce ƴan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun APC da PDP ba sa ba shi tsoro a aniyarsa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments