Daga DANTALA UBA NUHU KURA
An bukaci Al’umma musamman matasa da su Kaucewa dabiar nan ta rungumar daba da shan miyagun kwayoyi da zasu kawar musu da hankali, musamman a lokutan da ake gudanar da yakin neman zabe.
Bukatar hakan ta fito ne daga bakin Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Kiru Alh Muktari Isyaku lokacin taron Wayar Dakan Alumma Musamman ‘Yansiyasa Da Matasa Illolin Shaye-Shayn Miyagun Kwayoyi da haramcin Bangar Siyasa a Addinin Musulunci wanda kungiyar wayar da kan matasa ta shirya a karamar Hukumar Kura.
Yayin taron Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Kiru Alh Muktari Isyaku da Dattijo Alh Abubakar Maimai Wanda Shine Babban Jagora a Karamar Hukumar Kiru Sun Bayyana Farin Cikinsu Ga ayyukan Kungiyar Wayar Dakan Alumma Kan Hana Amfani Da MaKamai Da Hana Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi
Anasa jawabin shugaban kungiyar na Jahar Kano Reshen Karamar Hukumar Kiru Comrd Ibrahim Jamilu Ahammad Kafin-Maiyaki da Kansilan Yalwa Jamilu Muhammad Ya Wakilta ya bayyana kadan daga Tarihin kungiyar da kuma dalilin kafa ta.
Shima Da Yake Nasa Jawabin Babban Jamii a Hukumar Hana Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi ta Jihar kano wanda Ke Kula Da Shiyar Kiru Ahammad Shattema ya bayyana Illolin Shaye-Shayen ga lafiya jiki da kuma Addinin Musulunci
A karshe yayi Kira Ga Iyaye Wajan Kula Da Tarbiyar Yayan su tare da saka ido ga Irin Abokan Da Suke Maaamala Dasu Sannan ya roki ‘Yansiyasa Dasu Kaucewa Bangar Siyasa Wajan Amfani Da Rabawa Matasa Kwayoyi Da Mungan MaKamai
Ya Kuma Yiwa Yayan Kungiyar Da Suka Shirya Taron Fatan Alkhairi