Kamfanin man Najeriya na NNPC yace ya gano wata barauniyar hanya da aka yi shekaru kimanin tara ana satar danyen man kasar.
Jaridar The Cable tace shugaban kamfanin NNPC Limited, Mele Kyari ne ya yi wannan jawabin a gaban ‘yan majalisar tarayya.
Kyari ya shaidawa kwamitin harkar mai da gas na majalisar dattawa da na wakilai cewa a kokarin da suke yi an gano barawon but u turn mai wanda andauki shekaru da shimfida shi.
Barayi suna amfani da wannan bututu mai tsawon kilomita 4, suna satar danyen mai daga teku.
Yace gwamnati tana asarar gangar danyayan Mai 600, 000 a kowanne yini,
“An yi shekaru fiye da 22 ana satar danyen mai a kasar nan, amma sabon salon da aka dauka a ‘yan kwanakin bayan nan ya zarce na da.
Kamfanin UGC da Tashoshin Brass, Forcados, da na Bonny ba sa hako komai a yanzu; dalilin kuwa shi ne muna asarar ganguna 600, 000 a kowace rana.” – Mele Kolo Kyari
Shugaban kamfanin NNPCL yana cewa sun hada-kai da jami’an tsaro, suna kokarin maganin masu yi wa tattalin arzikin kasa illa. A wannan yunkuri da aka yi a makonni shida da suka gabata, Kyari yace sun rufe matatun danyen mai 395 da suke aiki ba tare da an san da zamansu ba.