Koriya ta Kudu ta bayar da rahoton cewa, Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami a yankin da ke tsakanin su.
A cikin sanarwar da sojojin Koriya ta Kudu suka fitar, an bayyana cewa an harba harsasai 100 daga gabar tekun yammacin Koriya ta Arewa sannan kuma an harba harsasai 150 daga gabar tekun arewacin kasar.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa harsasan ba su isa yankin ruwan Koriya ta Kudu ba, amma sun fada cikin yankin da ke tsakanin kasashen biyu da aka kaddamar a shekarar 2018.
A ranar 13 ga watan Oktoba, Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un ya jagoranci gwaje-gwajen makamai masu linzami masu cin dogon zango, wadanda ya bayyana a matsayin nuna nasarar fadada karfin sojojinsa a Fannin nukiliya da shirye-shiryen “yakin gaske”.
Koriya ta Arewa a cikin sanarwar da ta fitar a baya, ta yi ikirarin cewa gwajin makami mai linzamin da ta yi kwanakin nan na karkashin “halatattun aiyukan kariya”.
Makamin lizamin da Koriya ta Arewa ta harba a ranar 4 ga watan Oktoba, ya ratsa arewa maso gabashin Japan a karon farko tun shekarar 2017 kuma ya fada tekun Pacific.
An san cewa gwamnatin Pyongyang ta gudanar da gwaje-gwajen makamai masu linzami sama da 20 a wurare daban-daban tun daga farkon shekarar 2022, wanda ya saba wa kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.