Shugaban shashin Hausa ta Radio France RFI Sophie Bouillon tace zata bayar da muhimmanci wajan kulla kyakkyawar alaka tsakaninta Masarautar Kano.
Sophie Bouillon ta bayyana hakan ne a wata ziyara data kai fadar Masarautar Kano a ranar Larabar nan, a cigaba da ziyarar data kawo nan jihar Kano.
Tace ga yadda taga abubuwan tarihi da al’ada a masarautar ta Kano ya tabbatar da cewa tsohuwar Masarauta ce da tarike al’ada da ababan tarihi.
Shugabar sashin Hausa ta gidan Radio France tace zatayi duk abunda ya kamata wajan cigaba da kulla kyakkyawar alaka da yada manufofi da al’adun gargajiya na Masarautar ta Kano.
Ta yabawa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa irin hadin kai da goyon baya da yake baiwa kafofin yada Labarai na cikin gida da kuma na kasashen waje.
Da suke zagayawa da ita was bangarori na fadar Babban Sakataren Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Haruna Kwaru da kuma Sakataren yada Labarai na masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa sun godewa shugabar Sashin Hausa ta gidan Radio France RFI Sophie Bouillon bisa wannan ziyara data kawo masarautar.
Inda kuma suka bata tabbacin hadin kai da goyon baya domin cimma kudurce kudurcen da tazo dashi domin samun Nasarar da ake bukata.