Yadda hukumar Hisbah ta tarwatsa tawagar yan Daudu tare da kama uwar dakin su a gidan Rawa da tanbele na Ali Jita

Hukumar hisbah ta jihar Kano ta Kai samame shahararren wurin taron buki na Ali jita tare dayin nasarar dakile auren jinsi tsaknin wasu yan daudu biyu

Babban kwamandan hisbah shiek Haroon Muhammad  sani ibn sina yace yan daudu masu suna Mujahid da Abba sunyi nasarar tserewa amma an kama uwar dakinsu wacce tashirya bukin ranat haihuwarta Mai suna Salma Fulani

AA Zaura yayi alwashin bayar da goyon baya ga kungiyoyi masu tallata shi

Cutar Kwalara ta hallaka fiye da mutane 20 a jihar Cross River

Sheik ibn sina yace sunyi nasarar kamo yammata goma shatara yayin da mazan da suke wurin suka tsere amma anyi nasarar kama Mai kulada gidan shirya bukin

Babban kwamandan hukumar yace abin takaicin shine yadda yammatan suke da kananun shekaru amma sun bujirewa koyarwar manzon Allah s a w  da iyayen su suke aikata son zuciyarsu ya kuma bayyana cewar zasu gayyaci iyayen yaran da suke hannu a yanzu haka domin  ja musu kunne kafin su damka su a hannun su.

Kazalika  ya ce  mafi yawan yammatan ba haifaffun jihar Kano bane sun zo ne daga mabambantan jihohi don haka yayi kira ga iyayen dasu rinka kokarin sanin abokan mu,amillar ya’yan su don kaucewa haduwarsu da bata gari.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments