Rahotanni na nuni da cewa, an samu barkewar cutar kwalara a jihar Cross River dake kudancin Kasar nan, inda ya zuwa yanzu cutar ta haddasa mutuwar mutane kimanin 25.
A cewar jami’an lafiya na yankin, ya zuwa yanzu, an kwantar da mutane fiye da 30 da suka kamu da cutar.
Sai dai tuni Gwamnatin ta tura kwararrun ma’aikatan lafiya da kayan aiki zuwa kauyuka da cutar ta shafa, don hana cutar ci gaba da yaduwa.