Tsarin adashen Gata na Jigawa ya Burge Kungiyan Kwadagon jihar Niger
Tawagar kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Niger ta kai ziyarar gani da ido hukumar asusun adashen gata na fansho na jiha da kuma kananan hukumomin jihar Jigawa.
Jagoran tawagar wadda kuma shine shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na jihar Niger Kwamared Idris Lefene yace sun kai ziyarar ne domin kwaikwayon ayyukan hukumar da nufin aiwatar da irin sa a jihar Niger.
A cewar sa, sun ziyarci jihohi da dama domin ganin yadda suke aiwatar da tsarin biyan fansho amma tsarin biyan hakkokin fanshon jihar Jigawa ne yafi birgesu.
Comrade Idris Lefene, ya kara da cewar zasu yi amfani da dabarun jihar jigawa na ganin jihar Niger ta aiwatar da irin tsarin biyan fanshon
Kazalika, ya yaba da irin tarba da kuma tsarin gwamnatin jihar jigawa na biyan albashi da fansho akan lokaci.
A jawabin sa, Sakataren zartarwa na asusun adashen gata na fansho na jiha da kuma kananan hukumomin jihar jigawa, Alhaji Kamilu Aliyu Musa yace an kafa asusun ne a shekarar 2000.
Yana mai nuni da cewar, gwamnatin jihar ta jigawan take bada kaso 17 inda kuma ma’aikatan suke bada kaso 8.
Alhaji Kamilu Aliyu Musa yace babu wani ma’aikaci da yake bin asusun bashin kudin gratuity yayinda suke biyan fansho na wata wata kafin 10 ga kowane wata.
Tun da fari a nashi tsokacin, shugaban kungiyar kwadago na jihar jigawa Comrade Sunusi Alhassan Maigatari ya gabatar da tawagar tare da bayyana cewar kungiyar kwadago tana alhafari da asusun bisa yadda yake biyan hakkokin ma’aikata da fansho na wata wata akan lokaci.