Daga Kabiru A.Dukawa
Rundunar yan Sanda ta Kasa reshen jahar Kaduna, ta mika Kudi kimanin Naira miliyan 37,280 ga Iyalan jami’anta da suka rasa rayukan su a bakin aiki.
Kwamishinan yan Sanda na jahar Mudassiru Abdullah ne, ya gabatar da takardun Chakin Kudin a madadin Shugaban yan Sanda na Kasa, ga Iyalan yan Sandan a jahar.
Abdullahi yace, an bawa Iyalan yan Sandan su 23, kudin ne Naira miliyan 37,280,667 a matsayin wani shiri na biyan diyya ga jami’an da suka rasu a bakin aiki.
Kwamishinan ya bayyana wa Iyalai da sauran jami’an yan Sandan cewa, anyi musu wannan ne sakamakon gudun mawa tare da sadaukar da kai da suka yi, har yakai ga sun rasa rayuwar su wajen hidimtawa Kasa.
Daga karshe ya tabbatar musu da cewa, shugaban yan Sanda na Kasa yayi alkawarin kautata wa aikin jami’an rundunar, na wadanda suke aiki a yanzu haka da kuma wadanda suka rasa rayukan a cikin aikin a fadin Kasar nan.