Wata kungiya a Yakasai ta raba tallafi ga marayu da marasa karfi 150

An bukaci mawadata masu hanu da shuni da su Kara matsa kaimi wajan bayar da tallafin kayan Abinci da na sakawa ga marayu da marasa karfi musamman a wannan wata mai albarka na Ramadan.

Bukatar Hakan ta fito ne daga bakin Shugaban Kungiyar Mahammadu Sanusi na shafukan sada zumunta Sadam Nasir Na’ando yakasai  yayin da kingiyar ta bada Tallafin kayan abinci ga wasu daga cikin marayu harma da masu karamin karfi da kayan abinci a unguwar yakasai,

 

Kazalika yace kamata yayi masu hannu da shuni su rinka tallafawa masu karamin karfi domin rage musu radadin da suke ciki na rashin Abinci.

Wakilinmu Abdurashid Bello Imam daya halarci taron raban Tallafin ya rawaito cewar akalla mutane dari da hamsin ne suka sami wannan Tallafin.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments