Gidauniyar Albirru wattaqawa, ta gudanar da rabon kayan Abinci ga marayu da Talakawa

Kwamatin Kungiyar albirru wattaqawa foundation dake unguwar Danmaliki sun gudanar da rabon tallafin kayan abinci da kayan sakawa ga yara marayu a unguwar Danmaliki.

 

Wakiliyar Aksammedia ta ruwaito cewa Abubuwan da marayun suka rabauta da su na tallafin sun hada da  shinkafa ,masara gero, taliya, da kuma atamfofi.

 

A zantawar mu da  shugaban kungiyar alhaji shuaibu Danmaliki yace sun bayar da tallafin ga matune marasa karfi da kuma Marayu Domin a tafi kafada da kafada tsakanin mai shi da marashi musamman a wannan wata mai albarka na Ramadan dan a gudu tare a tsira tare.

 

Daga karshe mun zanata da wasu daga cikin wadanda suka rabauta da wannan tallafi  kuma sun nuna   jindadi  da godiya ga kunyiyar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments