Wasu kungiyoyi sun nemi Tinibu ya cire sunan El-Rufai daga jerin ministotin sa

Gamayyar kungiyar masu karatu da haddar Al-Qur’ani sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin minista domin gaskiya, adalci, zaman lafiya da dorewar kasar.

Daraktan kula da harkokin ilimi a wata Gidauniya ta Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Bauchi a madadin malaman, Sheikh Sidi Aliyu Sise, ya bukaci Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan sannan kada ya rantsar da azzaluman yan siyasa.

Ya ce zabar El-Rufai da tantance shi da majalisar dokokin tarayya ta yi rashin adalci ne ga masu karatu da masu haddar Al-Qur’ani, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya dage cewa a cire sunan El-Rufai domin tabbatar da adalci, zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban kasa, rahoton The Sun

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments