Shugabannin soji na Jamhuriyar Nijar sun nada Ali Mahaman Lamine a matsayin sabon Fira Ministan kasar
Kakakin gwamnatin kasar shi ya bayyana haka a jiya Litinin 7 ga watan Agusta da dare a fadar shugaban kasa
Wannan na zuwa ne bayan kungiyar ECOWAS ta ba wa sojin kwanaki bakwai da su mika mulki ga Bazoum
Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Nijar shi ya sanar da haka a jiya Litinin 7 ga watan Agusta da dare inda ya ce Lamine tsohon ma’aikacin AfDB ne da ke aiki a kasar Chadi.